Masu kiwon dabbobi domin sayarwa sun koka kan yadda farashin dabbobi ya karye a kasuwar sayar da dabbobi ta Rimin Gado a jihar Kano, lamarin da suka ce na jefa su cikin damuwa yayin da ake dab da gudanar da bikin Babbar Sallah.
Wakilinmu Ahmad Adamu Rimin gado ya rawaito cewa masu sayar da dabbobin sun bayyana cewa duk da yadda suka yi tsammanin samun riba sakamakon kusantar lokacin layya, amma farashin dabbobin na ci gaba da sauka, abin da suka ce na neman kassara musu jari.
Sai dai a gefe guda, wasu daga cikin masu sayen dabbobin da nufin yin layya sun koka kan cewa har yanzu farashin dabbobin na da tsada, inda suka ce da yawa daga cikinsu na duba yiwuwar hakura da sayan dabbobin.
Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da mako guda a gudanar da bikin Babbar Sallah, lokacin da ake yawan cinikin dabbobi domin layya.
