Sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma sun ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ’yan bindiga biyar a wasu hare-hare da suka kai a Jihohin Zamfara da Katsina.
Rundunar sojin ta ce an ceto mutanen ne a hanyar Bagega zuwa Kawaye da ke Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara bayan da jiragen yaƙi da sojojin ƙasar nan ya kai hari kan maɓoyar ’yan bindiga.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya ce waɗanda aka ceto sun fito daga yankuna daban-daban a jihohin Zamfara, Sakkwato da kuma Kebbi.
A wani samame na daban da aka kai Zamfara, sojoji sun kashe ’yan bindiga biyu a yankin Maradun zuwa Gidan Dan Jaja tare da lalata sansanoninsu.
- An samu rikici tsakanin Sojojin dake gadin kamfanin shinkafa na Fortune Rice Mills Limited dake Sharada da hukumar tabbatar da bin dokokin muhalli ta kasa (Nesrea)
- Sojojin sun kashe ’yan ta’adda huɗu tare da ƙwato makamai da kayan aiki a dajin Sambisa
- Mayakan Boko Haram Sun Kashe Wani Kwamandan Sojoji Da Karin Sojoji Shida A Jihar Borno
Haka kuma sun ƙwato bindigogi ƙirar gida da babura huɗu
A Jihar Katsina kuwa, sojoji sun daƙile wani hari da ’yan bindiga suka yi a Ƙaramar Hukumar Matazu.
A yayin musayar wuta, an kashe ’yan bindiga uku tare da ƙwato babura da alburusai.
Sojojin sun ce ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe na da alaƙa da ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Muhammad Fulani.
