Ana fargabar cewa a kalla mutane 16 ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka ɓace, bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai ƙauyen Kiliya da ke Ƙaramar Hukumar Dutsinma ta Jihar Katsina.
Wata majiya daga yankin ta bayyana wa jaridar Daily Trust cewa harin ya faru ne a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan mazauna ƙauyen sun kammala sallar Juma’a kuma suna cikin murnar Sallah.
Majiyar ta ce da farko an hango wasu ‘yan bindiga biyu a kan babur, lamarin da ya sa mutane su ka fara gudu don tsira da rayukansu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce har zuwa lokacin ba su samu rahoton harin a hukumance ba, amma ya yi alƙawarin bin diddigin lamarin da zarar rahoton ya isa ga rundunar
