Akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka kai a wasu ƙauyuka a jihar Katsina.
An kai hare-haren ne a ƙauyukan Jikamshi da Gwalgoro da ke ƙananan hukumomin Musawa da Kankia.
Rahotanni sun ce harin na baya-bayan nan ya faru ne a kasuwar Jikamshi da yammacin ranar Litinin, inda ‘yan bindiga suka bude wuta kan jama’a yayin da ‘yan kasuwa ke rufe kasuwanninsu, suka kashe mutane da dama.
Wannan hari ya biyo bayan wasu hare-hare daban-daban da aka kai a yankunan, wanda ya ƙara yawan waɗanda suka mutu zuwa 24.
Sai dai a wani bangare, an rawaito cewa dakarun soji sun kashe kusan ‘yan bindiga 45 a wani artabu da suka yi da su a ƙaramar hukumar Danmusa.
