Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar Cleanwave Green Club ta horas da daliban makarantar Firamare ta Sagir Koki Ilimin tsaftar muhalli da sarrafa shara.
An gudanar da bayar da horon ne a harabar makarantar gwamnatin dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar Birnin Kano.
Sakataren Ilimi na karamar hukumar Birnin Kano kwamaret Nura Sulaiman, ya ce gwamnati zata cigaba da tallafawa makarantu da horas da dalibai bangarori daban daban na ilimi.
Shima shugaban sashen kula da kananan makarantun sakandire na karamar hukumar Birni Alhaji Abbas Ado, ya buƙaci iyaye su tabbar ‘ya’yansu na kammala karatu har zuwa gaba da sakandire.
An ƙaddamar da kidayar makarantu ta shekarar karatu 2025/2026 a Kano domin inganta tsare-tsaren ilimi
A nata bangaren shugabar makarantar karamar sakandire ta Injiya Sagir Koki dake unguwar Tukuntawa Hajiya Ummu Zaitun Abdullahi Abbas ta bukaci gwamnati ta rungumi kungiyoyi dake tallafawa ilimi tare da tallafa musu.
Ta kuma nemi iyaye su tabbatar suna kai ‘ya’yansu makaranta.