Akalla mutane 37 ne su ka mutu ya yin da sama da 3,000 su ka kamu da cutar kwalara a kananan hukumomi bakwai na jihar Borno a watan Mayun nan.
Sakataren zartarwa na hukumar bayar da agajin lafiya ta jihar Borno Dakta Saleh Kaza ne ya tabbatar da alkaluman a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din data gabata, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban hadari ga lafiyar al’umma da ke bukatar daukar matakan gaggawa.
Dr. Kaza ya ce an samu rahoton bullar cutar ne a ranar 1 ga watan Mayu, kuma aka tabbatar da ita a ranar 4 ga watan na Mayu, yana mai cewa alkaluman sun shafi tun daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa ranar 29 ga watan na Mayu, inda sama da mutane 3,000 su ka kamu da cutar, yin da mutane 37 su ka mutu a unguwanni 36 a kananan hukumomi bakwai da abin ya shafa.
Dr Kaza ya bayyana cewa a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan an samu sabbin mutane sama da 100 da su ka kamu da cutar, inda karamar hukumar Maiduguri ta fi kowacce karamar hukuma kamuwa da cutar, inda mutane fiye da 2,000 su ka kamu da ita.
Ya shawarci mazauna yankin da su kula da wanke hannayensu da ruwa da sabulu akai-akai, gujewa bahaya a fili, zubar da shara barkatai, da kuma tsaftace abinci.
Dr Kaza ya bayyana cewa gwamnati tana kokarin ganin an samar da allurar rigakafin cutar kwalara a jihar nan ba da dadewa ba,Sai dai ya jaddada cewa allura ba za ta taba maye gurbin tsaftar muhalli da ta jiki ba.
