Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin ƙarfafa wayar da kan ɗalibai game da illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, a ƙoƙarin ta na marawa yunkurin gwamnatin jihar baya wajen yaƙi da matsalar tare da samar da ingantaccen yanayin koyo ga ɗalibai.
Shugaban kwalejin, Dr Kabir Ahmad Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce an kafa kwamitin ne domin shirya tarurrukan wayar da kai, bitoci da sauran shirye-shiryen ilmantarwa, wadanda za su sanar da ɗalibai illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da tasirinsu ga karatu, lafiya da makomarsu.
Dr Gwarzo ya ce kwamitin zai yi aiki tare da shugabannin ɗalibai, malamai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa saƙonnin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi sun isa ga kowane ɗalibi a faɗin kwalejin.
A cewar Dr Gwarzo, manufar shirin ya yi daidai da manufar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kare matasa daga illolin haramtattun ƙwayoyi.
Shugaban kwalejin ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da wasu buƙatu da kwalejin ta gabatar domin inganta yanayin koyarwa, inda ya ce cikin amincewar akwai gina ɗakin kwanan ɗalibai masu buƙata ta musamman, domin samar musu da muhalli mafi dacewa da karatu da rayuwar makaranta.
