
Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC, Mahmud Sadisu Buba wanda aka fi sani da Abin Al’ajabi, na fuskantar yiwuwar hana shi tsayawa takara bayan wasu takardu sun nuna cewa an haife shi ne a shekarar 2010.
Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa takardun NIN da fasfo dinsa sun nuna ranar haihuwarsa ita ce 27 ga Agustan 2010, wanda ke nufin zai cika shekaru 16 ne kawai a watan Agustan 2026, sabanin ikirarin da ya yi cewa ya haura shekaru 25 da kundin tsarin mulki ya tanada domin neman kujerar majalisar wakilai.
Lamarin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce tun bayan da ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar APC, inda aka rika yada hotunansa tare da manyan ‘yan siyasa ciki har da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.
A halin yanzu, an kai karar sa gaban kwamitin daukaka kara na APC kan zargin bayar da bayanan karya dangane da shekarunsa, takardun shaida da kuma bayanan karatu.
Masu karar sun bukaci jam’iyyar ta binciki takardunsa tare da neman tabbatarwa daga hukumomin NIMC, WAEC da NECO, sannan su nemi a hana shi shiga zaben fidda gwani idan aka tabbatar da karyar bayanai.
