Jirgin farko ɗauke da wasu baƙin haure ƴan asalin yammacin Afirka da aka kora daga Amurka a ƙarƙashin wani shirin Shugaba Donald Trump ya sauka a Saliyo ranar Laraba.
Baƙin haure da dama ne yanzu haka ke kan layi domin tiso keyarsu zuwa wasu ƙasashe da Amurka ta cimma yarjejeniya da su wajen karɓar wadanan mutane da jam’ian hukumar yaki da shige da fice ta kama a Amurka.
Saliyo a hukamnce ta ƙarbi bakin haure 25 ƴan asalin ƙasashen yammacin Afrika, acewar wata sanarwar da ministan harkokin wajen Saliyo Timothy Musa Kabba ya fitar.
Da saukar waɗanan baƙin haure a filin tashi da saukar jirage na Saliho,an hango ‘ƴansanda da likitoci da jami’an gwamnati da membobin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ke kula da baƙin haure ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) da suka tabbatar da isowar wadanan mutane tare da ba su kulawa da ta dace kamar yada dokokin ƙasa da ƙasa suka yi tanadi.
A wasu alkaluma da ake da su Amurka za ta dawo da kusan baƙin haure 300 ƴan asalin yammacin Afrika da yanzu haka Amurka ta riga ta tanttance ƙasashen da za a tisa keyarsu.
A hukumance minstan harkokin wajen Saliyo Timothy Musa Kabba ya shaidawa manema labarai cewa, ƙasar za ta ba su kwanaki 90 bayan haka suna da zabi na komawa ƙasarsu ta asali.
Wasu ƙasashe, kamar Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo, sun karɓi baƙi daga wasu nahiyoyi, ciki har da Latin Amurka.
