Ghana ta dakatar da ɗakko ‘yan kasar ta daga Afrika ta Kudu saboda tangarɗar da aka fuskanta dai dai lokacin da aka samu lafawar hare-haren da fusatattun ƴan ƙasar ke kaiwa baƙi ƴan ƙasashen Afrika.
Ghana ta ce ta dakatar da aikin kwaso ƴan ƙasar ta fiye da 800 da ke zaune a Afrika ta Kudun ne, bayan fitar wani faifan bidiyon da ke nuna yadda ake cin zarafin wani ɗan Ghana.
Bidiyon ya nuna yadda ƴan Afrika ta Kudu suka kai wa ɗan Ghanan mai suna Emmanuel Asamoah hari, a wani sabon gangami da suka soma na nuna ƙyamar baƙi baƙaƙen fata da ke zama cikin ƙasar su.
A farkon watan nan ne, ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta sanar da shirin fara kwaso ƴan ƙasar ta daga Pretoria daga wannan alhamis ɗin.
To sai dai ma’aikatar ta ce shirin ya samu tangarɗa ne sakamakon yawan mutanen da kuma ƙa’idoji da mahukuntan Afrika ta Kudu suka kindaya.
