Babban ɗan tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdulaziz Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
Abdulaziz na neman wakiltar mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a jihar Kano.
Duk da kasancewar mahaifinsa ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC tsawon shekaru, Abdulaziz ya daɗe yana cikin sahun masu biyayya ga tafiyar siyasar Kwankwasiyya, wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna Abdulaziz yana tattaunawa da Kwankwaso jim kaɗan bayan karɓar fom ɗin takarar, inda rahotanni ke cewa ya yi masa bayani kan burinsa na siyasa da kuma shirinsa na fafatawa a babban zaɓe mai zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa Abdulaziz ya daɗe yana nesanta kansa daga tsarin siyasar mahaifinsa, yana kuma bayyana goyon bayansa ga tafiyar Kwankwasiyya a fili.
Hakan ya ƙara bayyana ne bayan rikicin da ya taɓa shiga da mahaifiyarsa, Hafsat Umar Ganduje, inda ya kai ƙorafi kan ta ga EFCC bisa zargin karya wata yarjejeniya tsakaninsu.
Abdulaziz na neman kujerar ne inda ɗan’uwansa, Umar Abdullahi Ganduje, ya tsaya takara a ƙarƙashin APC a zaɓen 2023, amma ya sha kaye a hannun ɗan takarar NNPP, duk da cewa a lokacin mahaifinsu ne ke kan mulki a matsayin gwamnan Kano.
