Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar zaɓe INEC ta bayyana Usman Ahmad Ododo na jam'iyyar APC a...

Hukumar zaɓe INEC ta bayyana Usman Ahmad Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda lashe zaɓen gwaman jihar Kogi.

Date:

Hukumar zaɓe INEC ta bayyana Usman Ahmad Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda lashe zaɓen gwaman jihar Kogi.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓe na hukumar INEC a jihar Kogi, Johnson Ozoemenam Urama ne ya tabbatar da nasarar ta Ododo a sanarwar da ya bayar cikin daren jiya Lahadi.

INEC ta ce Ododo na APC ya samu ƙuri’a 446,237, saboda haka shi ne halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar, kasancewar shi ne ya samu ƙuri’a mafi rinjaye.

Muritala Yakubu Ajaka na jam’iyyar SDP shi ne ya zo matsayi na biyu, inda ya samu ƙuri’a 259,052.

Dino Melaye na jam’iyyar PDP ne ya zo na uku da ƙuri’u 46,362.

Sai kuma Abejide Leke Joseph na jam’iyyar ADC wanda ya samu ƙuria 21,819.

Gabanin sanar da nasarar Ododo, hukumar zaɓen ta ce ba za a gudanar da zaɓuka a rumfunan da ta dakatar da zaɓe ba a ranar Asabar.

An dakatar da zaɓe a wasu rumfuna ne bayan samun bayanai na almundahana, inda aka ga cikakkun takardun sakamako tun gabanin fara kaɗa ƙuri’a.

Sai dai a bayanin da jami’in hukumar INEC ya yi gabanin sanar da wanda ya yi nasara, ya ce yawan katin zaɓe da aka karɓa a dukkanin wuraren da aka soke zaɓe ya tsaya ne a 16,247.
Hakan na nufin koda an sake zaɓen ba zai shafi nasarar ɗan takarar da ke gaba a yawan ƙuri’a ba.

Ahmed Ododo ya bai wa mai biye masa ratar ƙuri’a 187,185.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...