37.6 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiHukumar alhazai ta kasa ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2023.

Hukumar alhazai ta kasa ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2023.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hukumar alhazai ta kasa ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2023.

 

Hukumar kula da aikin hajji ta kasar nan (NAHCON), ta ce ta fara shirye-shiryen aikin hajji na 2023 domin kaucewa matsalolin da aka samu a aikin hajjin bana.

 

Nahcon ta ce ta kuma dauki matakin soma shirye-shiryen ne don samun nasara yayin hajjin badi ba tare da samun matsaoli ba.

 

Hukumar jin dadin alhazai ta baiwa maniyyata mako guda su cika kudadensu

 

Shugaban hukumar na kasa, alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a wajen taron lakca da mika lambar yabo dangane da hajjin bana a Abuja.

 

Shugaban hukumar ya samu wakilcin daraktan gudanarwa na hukumar, Dakta Ibrahim Sodangi, inda ya ce sun soma shirye-shiryen ne daga lokacin da aka kammala hajjin bana tun kafin ma su baro Saudiyya.

 

Ya ce tuni hukumar ta jin dadin alhazai ta gana da masu ba da masauki don tanada wa ’yan najeriya masauki mai inganganci yayin hajji mai zuwa.

 

Haka hazalika, ya ce hukumar na da kudurin shirya babban taro na kasa da kasa domin ganawa da masana daga sassa daban-daban don cim ma nasarar a hajjin badi.

 

Daga bisani, Hassan ya yaba wa IHR bisa kokarin da ta yi wajen shirya taron don karrama ma masu ruwa-da-tsaki a harkokin hajji.

Latest stories