Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMatsalar tsaro: DSS ta umarci ASUU ta janye yajin aiki

Matsalar tsaro: DSS ta umarci ASUU ta janye yajin aiki

Date:

Hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS ta bukaci kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU da ta janye yajin aikin da takeyi saboda dalilan tsaro.

 

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kotun da’ar ma’aikata ta baiwa kungiyar malaman jami’ar umarnin janye aiki da suka shafe watanni bakwai suna yi saboda rashin cika musu alkawarukan su da gwamnatin tarayya tayi.

 

Daraktan hukumar dake jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir, ne ya bukaci hakan yayin taron shugabanin hukumomin tsaro na arewa maso gabashin kasar nan da akeyi duk bayan watanni ukun shekara a Damaturu.

Rashin Tsaro: An gudanar da sauka 2,444 a Kano.

Ya ce yajin aikin da ya durkusar da jami’o’in kasar nan na da tasiri kan sha’anin tsaro.

 

Yunusa Abdulkadir, y ace ya kamata kungiyar malaman jami’ar suyi na tsanaki kan kalubalan da arewa maso gabashin kasar nan ke fuskanta tsaron shekaru a sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga.

 

Daraktan hukumar ya kuma bukaci da asamar da asibitin lura da masu matsalar kwakwalwa don kula da wadanda suka samu matsala a sanadiyar rashin tsaro.

 

Ya ce rashin yin hakan zai ta’azzara matsaloli ga wadanda abin ya shafa wanda kuma hakan wata barazana ce ga matsalar tsaro a jihar.

Latest stories

Related stories