Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNajeriya na fama da ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 10-NEMA

Najeriya na fama da ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 10-NEMA

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ambaliyar ruwa a jihohi 27 daga cikin jihohi 36 na kasar nan da babban birnin tarayya Abuja, ta shafi mutane rabin miliyan da suka hada da 100,000 da suka rasa matsugunansu, yayin da fiye da 500 suka jikkata.

Kamfanin dalillacin labarai na Reuters ya bayyana cewa sama da mutane 300 suka mutu a shekarar 2022 ciki har da akalla mutane 20 a wannan makon.

Har ila yau, bala’in ya lalata dubban gonakin noma, abin da ke kara tsananta fargabar rashin abinci a kasar nan.

Tun daga shekarar 2012, wannan itace ambaliyar ruwa mafi muni data halaka mutane da dama,” in ji Manzo Ezekiel, mai magana da yawun hukumar kula da jinkai ta kasar nan.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...