31.9 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiKwale-kwale ya kife da mutane 9 a Madobi

Kwale-kwale ya kife da mutane 9 a Madobi

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

 

Ana fargabar mutane shida sun mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a garin Kanwa da ke karamar hukumar Madobi.

 

Al’amarin ya faru ne cikin daren Larabar nan a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga garin Kura.

 

A cewar shaidun gani da ido an samu nasar tsamo mutune uku da ransu, ya yin da ake ci gaban da neman ragowar shidan.

 

Dayyabu Muhammad guda ne cikin wadanda suka rasa iyalansu a hadarin, ya ce ya rasa matarsa da ‘yan yansa maza biyu.

 

Ya ce sun rabu da matar ne za ta je gaishe da iyayenta sai labari aka bashi cewa kwale-kwalen ya kife da su.

 

“Mun rabu da ita za ta tafi gaida iyayenta, da ‘ya ‘yana biyu sai labari aka bani kwale-kwale ya kife da su.

 

“Mun je wajen munyi ta bincike a mma har gari ya waye ba mu samo su ba yanzu dai mun zubawa sarautar Allah Ido.” A cewarsa.

 

Da yake jawabi dangane da iftilain Lawan Yahya a madadin shugaban karamar hukumar Madobi ya ce wannan ibtil’ine babba.

 

Shugaban wanda ya ce  hadarin iftila’i ne mai tada hankali, inda ya bukacesu su mai da komai ga Allah madaukaki.

 

Lawan Yahya ya bukaci da su dinga kaucewa shiga ruwan musamman a wannan lokaci da ake fama da Ambaliyar ruwa.

 

Har yanzu dai ba a kai ga samo gawarwakin wadanda ake fargabar sun mutu ba.

 

Latest stories