Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu Sunan Osinbajo A Jerin Yan Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu

Babu Sunan Osinbajo A Jerin Yan Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu

Date:

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo baya cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.

 

Jerin sunayen mutane 422 da James Faleke, Sakataren Kwamitin yakin neman zaben ya fitar da safiyar yau Asabar ya kunshi wasu ‘yan takarar shugaban kasa da dama da suka kara da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gabatar a watan Yuni.

 

Wasu daga cikin wadanda ke cikin jerin sunayen sun hada da Cif Bisi Akande, Cif John Odigie-Oyegun, Cif Olusegun Osoba, Alhaji Tanko Yakasai, Zainab Asipita Ogundana da wasu 69 da aka bayyana a matsayin Yan kwamitin yakin neman zabe.

 

Hakan ya tabbatar da zargin da ake cewar akwai rashin jituwa tsakanin Osinbajo da tankarar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...