24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano Ta Yiwa Masu Zubar Da Shara A Hanya Allah Ya...

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Masu Zubar Da Shara A Hanya Allah Ya Isa.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Daga Muktar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta yiwa masu zubar da shara akan hanyoyi da titunan jihar Allah ya Isa.

 

Kwamishinan Muhalli Dr Ibrahim Getso ne yayi Allah ya isar yayin duban tsaftar Muhalli na karshen wata.

 

Getso ya ce abin takaici ne yadda jama’a suka mayar da hanyoyi wurin zuba shara.

 

Ya ce ko kadan gwamnati ba za ta lamunci cin kashin da jama’a ke yi a hanyoyin Kano ba.

 

” Gwamnati ita kadai ba za ta iya ba, akwai bukatar jama’a da kungiyoyi su shigo cikin wannan aiki,Mu hada kai domin a samu nasarar tsaftace muhallinmu, domin mu muke zaune a cikinsa.” A cewar Kwamishinan.

Latest stories