Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Buhari ya kaddamar da sabbin gine-gine a FCE Kano.

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin gine-gine a FCE Kano.

Date:

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin gine-gine na dakunan karatu da ofisoshi a kwalejin horas da malamai ta F.C.E dake nan Kano a ranar Juma’a.

 

Yayin kaddamar da gine-gine shugaba Buhari ya yabawa asusun tallafawa manyan makarantu na kasa (TETFUND) bisa yadda aka gudanar da aikin.

 

Buhari zai kai ziyara Maiduguri a ranar Alhamis

Shugaban wanda ya samu wakilcin Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibril Maliya, ya kuma yabawa ministan ilimi inda yace aikin zai taimaka wajen ciyar da ilimi gaba a jihar nan.

 

A nasa bangaren shugaban kwalijin horas da malaman ta FCE Kano Dakta Sadi Muhammad Surajo, ya mika godiyar sa bisa yadda gwamnati ta gudanar da aikin.

 

 

Da yake jawabi shugaban hukumar gudanarwar kwalejin Abdulmalik Mahmud, yace suna aiki tukuru don sanya shugaban kasa da ministan ilimi su amince da maida kwalejin zuwa Jami’a a jihar Kano.

 

 

Shugaban hukumar gudanarwar kwalejin horas da malaman ta Kano Abdulmalik Mahmud, yace duk da wannan aiki kwalejin na bukatar wasu aikace aikacen daga gwamnatin tarayya.

Latest stories

Related stories