24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta gano kwalejojin bogi 200 dake bada shaidar karatu na...

Gwamnatin tarayya ta gano kwalejojin bogi 200 dake bada shaidar karatu na NCE

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin tarayya tace ta gano makarantu da kwalejojin ilimi na bogi da suke bada shedar karatun NCE a kasar nan ciki har da jihar Kano.

 

Shugaban hukumar dake kula da kwalejojin ilimi na kasa Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle, ne ya bayyana haka yayin kaddamar da sabbin gine-ginen dakunan karatu a kwalejin horas da malamai ta FCE dake nan Kano wanda akayi a yammacin jiya Juma’ar.

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Masu Zubar Da Shara A Hanya Allah Ya Isa.

Ya ce akwai makarantun bogi da basu da rijista da gwamnati, fiye da dari biyu a kasar nan da suke bada shedar kammala karatun NCE.

 

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta hannun ministan ilimi zata bayyana makarantun nan bada jimawa ba, tare da rufe su baki daya.

 

Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle, ya ce tuni a ranar Juma’a suka mikawa kwamishinan ilimi na jihar Kano takadar da suke neman hadin kan gwamnati wajen rufe ire iren wadannan makarantu na bogi.

 

Ya ce zasu turawa kwamishinan ilimi na jihar nan sunaye da adadi da kuma guraren da makarantun bogin suke.

 

Shugaban hukumar dake kula da kwalejojin ilimin Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle, ya ce idan har gwamnatocin jihohi basu dauki matakin rufe makarantun ba to akwai shirye shirye da suke yi na daukar matakin da ya dace akai.

Latest stories