31.9 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiHajj 2022: NAHCON ta kammala dawo da alhazan bana

Hajj 2022: NAHCON ta kammala dawo da alhazan bana

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta kamala aikin dawo da alhazan da suka sauke farali a bana gida Najeriya.

Jirgin kamfanin Azman ne na karshe da ya taso daga jidda da alhazai 319 da ga jihohin Kano da Kaduna da kuma sauran jam’ina hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, da na NAHCON.

Jirgin ya tashi daga filin jirgin saman Jidda da misalin 12:00 na ranar jiya Lahadi zuwa nan gida Najeriya.

NAHCON ta baiwa wadanda ba su samu yin aikin Hajji ba Hakuri

HAJJIN BANA: Jihar Kano za ta fara dawo da Alhazan ta

Nayi aikin hajji a Kano ne don na debewa maniyyata kewa-Miniyyaci

Wannan dai shi ke nuna kawo karshen jigilar aikin hajjin bana da hukumar ta NAHCON ta yi.

Idan za a iya tunawa dai an baiwa kasar nan adadin kujeru 48,008 ga minyyatan kasar nan.

Sai dai hukumar ta NAHCON bata iya kwashe dukkanin maniyyatan zuwa kasa mai tsarki ba.

Latest stories