Saurari premier Radio
27.2 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnonin kasar nan sun bukaci Buhari ya karawa talakawa haraji

Gwamnonin kasar nan sun bukaci Buhari ya karawa talakawa haraji

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnonin kasar nan sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara harajin da talakawa ke biya.

Haka kuma sn bukaci a sanya haraji kan kowanne mutum da ke samun N30,000 a kowanne wata.

Jaridar Premium Times ce ta bankado wannan shawara da gwamnonin suka gabatar wa shugaban kasa lokacin wani taro da suka gudanar da zummar lalubo hanyar samar wa gwamnati karin kudaden kashewa.

Shawarar gwamnonin ta kuma kunshi aiwatar da rahotan Kwamitin Stephen Oronsaye wanda ya bukaci rufe wasu ma’aikatun gwamnati da basu da tasiri ko kuma wadanda ayyukansu ke cin karo da na wasu ma’aikatu.

Haka kuma sun shawarci  Shugaban  kasar da ya kori duk wani ma’aikacin da ya zarce shekaru 50 a duniya.

Wannan dai na zuwa ne yayin da kasar nan ke fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata, sakamakon matsalolin da suka addabi kasar.

Gwamnatin  Tarayya na da ma’aikata dubu 89 ne amma kuma tana kashe naira tiriliyan 4 da biliyan 100 wajen biyan su albashi da alawus alawus kowacce shekara daga cikin kasafin kudin naira tiriliyan 17 da ta ke yi a shekara.

Latest stories

Related stories