Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNa zama butulu idan na yi bakin cikin cire ni daga sarki-Sunusi...

Na zama butulu idan na yi bakin cikin cire ni daga sarki-Sunusi II

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sunusi II ya ce ya zama butulu indai ya nuna bacinsa so da nasani don  an tunbuke shi a matsayin sarkin Kano la’akari da irin mukaman da ya rike a rayuwasa.

 Sarki Sunusi ya bayyana hakanne ranar Asabar a wani taro fim din dabe da aka yiwa take da “Emir Sunusi: Truth In Time” da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Sarkin ya ce ya yi duk kokarin da zai yi ya ga ya bayar da gundumawarsa wajen gina kasa, saboda yadda ya dade a cikin gwamnati.

Ya ce ya yi aiki da Bankin UBA sannan ya tafi Bankin First Bank, sannnan ya rike gwamnan babban bankin kasa CBN ya kuma zama sarkin Kano na shekaru 6, yanzu kuma yana khalipah Tijjaniyya na kasa.

“Banajin Ubangiji ya hanani komai, dan haka bana da na sani’

“Shekaruna 61 a duniya a tsawon wadannan shekaru na rike mukamai da yawa ciki harda gwamnan babban bankin kasa CBN  da sarkin Kano.

“Idan na nuna bacin raina, to lallai na zama butulu, mutane nawa ne ke da burin samun dama koda daya ne da ga cikin wadannan abubuwa da na cimma.” A cewar sarki Sunusi.

Latest stories

Related stories