Saurari premier Radio
27.5 C
Kano
Friday, July 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan bindiga sun sa ce Ango da Amarya a Katsina

‘Yan bindiga sun sa ce Ango da Amarya a Katsina

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wasu ’yan bindiga sun sa ce wata amarya da angonta bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke Katsina.

A cewar BBC mazauna unguwar na cewa ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1 da minti 25 na daren Asabar, inda suka shafe tsawon sa’a guda su na harbe-harbe.

Sun shaida cewa ’yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.

Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ’yan bindigar sun fi karfinsu.Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa, ’yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura dauke da bindigogi suna harbe-harbe.

Mutumin ya ce ’yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga, lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da jikkatar wasu biyun.

Ya kuma ce baya ga sabbin ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ’yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kubutar da amarya da angon.

SP Gambo ya kuma ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin Karamar Hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ’yan bidiga.

Kazalika, ya ce a yankin Karamar Hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...