Ahmad Hamisu Gwale

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 2 da nema a wasan farko na gasar Firimiyar Ingila ta shekarar 2022/2023.
Fafatawar dai ta gudana a filin wasa na Selhurst Park a ranar Juma’ar nan.
Dan wasa Gabriel Martinelli shine ya Fara zura kwallon farko a minti na 20 bayan samun tai mako daga sabon dan wasan Arsenal Oleksandr Zinchenko.
Sai Kuma kwallo ta biyu da dan wasa Marc Guehi ya zura a ragar kungiyarsa wato Own goal.
Wanda Anthony Taylor ya jagorancin alkacin wasan da kungiyoyi biyun suka kai ruwa rana.
Wasanni: Kano Pillars zata kara da Wikki Tourist a gasar firimiya ta kasa
A kalla dubban magoya baya ne dai suka halarci kallon wasan da shine na farko na kakar shekarar 2022/2023 da aka fara.
Sauran wasannin da zasu gudana a ranar Asabar 6 ga watan Agusta sun hada da….
Fulham da Liverpool
Leeds United da Wolverhampton Wanderers
Newcastle United da Nottingham Forest
Tottenham da Southampton
Bournemouth da Aston Villa
Everton da Chelsea
Yayin da Ranar Lahadi 7 ga watan Agusta
Manchester United da Brighton & Hove Albion
Leicester City da Brentford
West Ham United da Manchester City