Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban kasa Tinubu zai kaddamar da aikin gina katafaren titi daga Sakkwato...

Shugaban kasa Tinubu zai kaddamar da aikin gina katafaren titi daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas.

Date:

Ministan Ayyuka, Injiniya Dave Umahi, ya ce a wata mai zuwa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da aikin gina katafaren titi daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas.

 

Umahi ya ce a watan Afrilu Shugaba Tinubu zai kaddamar da aikin titin mai tsawo kilomita 1,000 a Jihar Kebbi.

Da yake tattaunawa a Jihar Kebbi da masu ruwa da tsaki kan rukunin farko da na biyu na aikin jihohin Kebbi da Sakkwato, Umahi ya shaida musu cewa aikin zai fara ne daga bangaren da ke da nisa kilomita 258 a jihar.

Ya kara da cewa titin yana daga cikin aiki gina titin Trans-Sahara da zai hada Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Ministan ya ce an shafe shekaru 48 ana magana a kan gina titin domin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da sauran kasashen Afirka, amma ba a yi ba sai da Tinubu ya hau mulki.

Da yake jawabi, Gwamna Nasiru Idris, ya ce batun aikin titin ya faranta wa al’ummar jihar rai, wanda zai taimaka wajen cimma burin ’yan kasa da dama.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...