Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWasanni: Kano Pillars zata kara da Wikki Tourist a gasar firimiya ta...

Wasanni: Kano Pillars zata kara da Wikki Tourist a gasar firimiya ta kasa

Date:

A cigaba da fafatawa a gasar Premier ta kasar nan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata kece raini da takwararta ta Wiki Tourist.

Gwamnatin Kano zata siyawa Katsina United sabuwar mota

Za ayi wasanne a ranar Lahadi 12 ga watan da muke ciki da karfe hudu na yamma.

Kano Pillars ce zata karbi bakuncin Wikki Tourist din a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata sai dai za ayi wasanne ba tare da ‘yan kallo ba kamar yadda hukumar dake shirya gasar league ta kasa (LMC) ta bada umarni.

A baya dai hukumar ta maida Kano Pillars cigaba da fafata wasanta na cikin gida a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja bayan da magoya bayan kungiyar suka farmaki ‘yan wasan Katsina United kafin yanzu a sassauta musu hukuncin na cigaba da yin wasa a gida amma batare da ‘yan kallo ba.

A wani labarin kuma an bude musayar ‘yan wasa dake buga kwallo a kungiyoyin premier na kasar Ingila a Juma’ar nan.

Wannan na zuwa ne yayin da kwantiragin ‘yan wasa da dama ke karewa a kungiyoyin su inda wasu suka sanya hannu a sabbin kwantiragi da wasu kungiyoyin.

Kuma ana sa ran za a rufe musayar ‘yan wasan a ranar Alhamis daya ga watan Satumba mai zuwa.

An dai baiwa kungiyoyin kwallon kafar Ingila damar daukar ‘yan wasa tun bayan kammala wasannin su na karshe na kakar bana.
Tuni dai kungiyar Manchester United ta tabbatar da cewa ‘yan wasanta goma sha daya ne zasu bar kungiyar daga karshen watan Yunin da muke ciki.

A wani cigaban kuma rahotanni na cewa Manchester United na shirin daukar dan wasan tsakiyar Liverpool Alex Oxlade-Chamberlain Dan wasan na kasar England yana da damar barin Liverpool a wannan kakar.

Haka zalika jaridar talkSPORT ta ce, United na son daukar dan wasan akan kudi Yuro miliyan 10.

Sai dai, Rahotanni sun bayyana cewa West Ham da Aston Villa suma suna kan gaba wajen neman daukar dan wasan.

Latest stories

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...