35.9 C
Kano
Monday, March 20, 2023
HomeLabaraiWani yayi barazanar sace makwafcinsa a Kano ko ya biya miliyan 100.

Wani yayi barazanar sace makwafcinsa a Kano ko ya biya miliyan 100.

Date:

Related stories

Muna cigaba da tattara bayanai game da gobarar kasuwar kurmi – SEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano ta...

APC ta shirya lauyoyinta domin tunkarar PDP da LP a kotu

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC...

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kama wani dakewa makwabcinsa Barazanar cewa zaiyi garkuwa dashi ko kuma ya biya Naira miliyan 100.

 

Lamarin ya faru ne a garin Makadi dake karamar hukumar Garko.

 

Isa Musa wanda rundunar yan sandan ta kama, ya hada kai da abokinsa ne inda yake amfani da wayar tarho domin kiran makwabcin nasa don yin barazana gareshi.

 

Wanda rundunar ƴan sandan Kanon ta kama yace ganin makwafcin nasa yayi da kudi, shiyasa ya hada kai da abokinsa don yi masa barazana.

 

Shima wanda akayiwa wannan barazanar yace da fari an naimi ya biya naira miliyan 100, amma daga bisani an karkare zai biya naira miliyan 2.

 

Yace sakamakon barazanar da aka yi masa, akwai ranar da babu wanda yayi bacci a garin Makadi, sai da jami’an ƴan sanda Suka kwana suna sintiri.

 

SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar yan sanda na jihar Kano, yace sun bibiyi masu laifin kuma sun chafke wanda ake zargi da aikata laifin, za’a kuma a gurfanar dashi a gaban kotu.

Latest stories