Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGanduje ya rushe wani ginin kasuwa da ake yi a kofar gidan...

Ganduje ya rushe wani ginin kasuwa da ake yi a kofar gidan Kadiriyya

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya rusa wani ginin kasuwanci a kusa da gidan fitaccen jagoran Darikar Kadiriyya, Marigayi Sheikh Nasiru Kabara.

Ginin, wanda ke wani fili mallakin Masarautar Kano, Gwamna Ganduje ya sa a rushe shi ne, saboda an yi shi  ba tare da sahalewar gwamnatin jihar ba.

Shugaban hukumar (KAROTA) kuma Shugaban Kwamitin Rusa Gine-ginen da aka Yi ba bisa ka’ida ba, Baffa Babba Dan Agundi ne ya jagoranci rushe ginin.

Bappa Babba  ya ce daga Gwamnatin Jihar Kano har Masarautar Kano babu wanda ya ba da izinin yin ginin.

“Ya kamata mutane su sani cewa yin ginin ya haifar da zargi tsakanin gwamantin Kano da masarauta, duk kuwa da cewa a cikinsu babu wanda ke goyon bayan yin ginin.

“Bayan gudanar da bincike, an gano cewa wasu masu son zuciya, wadanda kansu kawai suka sani ne suke da ginin.

“A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Ganduje ya ba da umarnin rushe ginin, tare da katange wurin domin mayar da shi dandalin wasan yara.

“Ragowar filin kuma za a ci gaba da amfani da shi wajen gudanar da zikirin Darikar Kadariyya kuma shi ma za a katange shi.”

Ya ce gwamnan ya sa a girke jami’an tsaro a koyaushe a wurin domin bayar da kariya ga yara masu wasa da iyayensu daga ayyukan bata-gari.

Dan’agundi ya gargadi mutane da su guji yin gine-gine ba bisa ka’ida ba, saboda Gwamnatin Jihar Kano, “Ta dauki matakin gurfanar da duk wanda ya aikata hakan a gaban kuliya.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...