33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabarai2023: PDP na kokarin sasanta ‘ya’yan ta gabanin zabe

2023: PDP na kokarin sasanta ‘ya’yan ta gabanin zabe

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

PDP tace shirye shirye sun yi nisa na tattaro kan yayan jam’iyyar, musamman wadanda aka batawa, domin sasanta tsakani su.

Wannan na daga cikin yunkurin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar gabanin tunkarar babban zaben 2023, domin fatan samun nasara.

Shugaban kwamatin amintattun jam’iyyar Sanata Walid Jibril ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a Litinin dinnan, inda yace zasu duk mai yuwuwa wajen hade kan yayan jam’iyar.

Ya kuma ce sun shirya ganawa da gwamnan River Nyensom Wike, da sauran wadanda aka batawa.

A cewar Sanata Walid, rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta bai kama kafar wanda APC mai mulki ke ciki ba, musamman batun tsayar da musulmi da musulmi takarar shugaban kasa da mataimaki.

Latest stories