Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiA shirya tunkarar ambaliyar ruwa-NIMET

A shirya tunkarar ambaliyar ruwa-NIMET

Date:

Hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET tace ‘yan Najeriya su shirya fuskantar mamakon ruwan sama daga yanzu zuwa watanni 2 masu zuwa.

Shugabanta Farfesa Mansur Baba Matazu ne ya bayyana hakan, da yake zantawa da gidan talabijin na Arise, game da ambaliyar ruwan da aka samu a sassan kasar nan.

Ko a Litinin din makon nan ma, rahotanni sun bayyana mutuwar wani yaro dan shekaru 3 da haihuwa sanadiyar ambaliyar ruwa a garin Bajoga dake jihar Gombe.

Farfesa Matazu yace tuni hukumar ta bayar da shawarwari kan yadda al’umma zasu kare kansu daga ambaliyar da akayi hasashen samu, amma basu dauka ba.

Ya koka da cewa har yanzu, mutane na cigaba da sare itatuwa da kuma zuba shara a magudanan ruwa, abubuwan dake taka rawa, wajen kawo ambaliyar ruwa.

Yace lallai akwai bukatar ‘yan Najeriya su dauki rahotannin hasashen yanayi da muhimmanci.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories