33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiINEC ta ja kunnen mutane game da shafukan hukumar na bogi

INEC ta ja kunnen mutane game da shafukan hukumar na bogi

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hukumar zabe ta kasa INEC tayi kira ga al’umma da su kauracewa shiga komar yan damfara da sunan yi musu rajistar katin zabe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Festus Okoye ne yayi kiran a wata sanarwa da ya fitar, yana mai tabbatar da rufe yin rajistar tun a Lahadin da ta gabata.

A cewar hukumar,  wasu marasa kishin kasa sun bude shafukan intanet na bogi da sunan hukumar, inda suke yaudarar al’umma da cewa gwamnatin tarayya ta amince da a ci gaba da yiwa jama’a rajistar, domin magance cunkoso a ofisoshin INEC.

Wannan ya biyo bayan cikar wa’adin rufe yin rajistar da INEC ta sanya.

Kafin haka dai, kungiyoyin fafutuka, sun nemi a tsawaita lokacin domin baiwa karin yan Najeriya damar mallakar katin zabe.

Latest stories