Ƙaramin Ministan Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware kuɗaɗe da suka kai biliyoyin naira domin kammala aikin titin Wuju-Wuju.
Ministan ya ce ware kuɗaɗen na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tabbatar da kammala muhimman ayyukan more rayuwa, musamman waɗanda za su inganta zirga-zirga da sauƙaƙa harkokin sufuri.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakiliyar Premier Radio, Amina Umar Kafinta, inda ya yi ƙarin bayani kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin ganin an kammala aikin.
Kammala titin na da muhimmanci wajen inganta zirga-zirgar ababen hawa, rage wahalhalun masu amfani da hanyar da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci a yankunan da aikin ya shafa.
