Tsohon shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Arc. Aminu Dabo, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.
Dabo ya bayyana matakin nasa ne ta cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugabancin jam’iyyar APC na mazabar Ɗambatta Gabas, da ke Ƙaramar Hukumar Ɗambatta a Jihar Kano.
Kafin ficewarsa, Aminu Dabo ya kasance shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Ɗambatta.
A cikin wasiƙar tasa, tsohon shugaban na NPA ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar bisa goyon baya, haɗin kai da kuma damar da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Sai dai, a cikin bayanan da aka bayar, ba a bayyana dalilin da ya sa Aminu Dabo ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ta APC ba.
