Barrister Abba Hikima Fagge, ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya hana shi ci gaba da fafutukar da yake yi, face mahaifiyarsa.
Abba Hikima ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta DCL, inda ya jaddada cewa har yanzu yana da cikakken imani da manufar tafiyar tasa, don haka ba ya ganin akwai dalilin da zai sa ya dakatar da ita.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu bai amince ya zauna da ko ɗaya daga cikin gwamnonin da suka nemi tattaunawa da shi ba.
A cewarsa, wasu gwamnoni sun tuntube shi, inda suka bayyana cewa akwai wasu abubuwa da yake buƙatar fahimta game da wannan fafutuka, kuma suna son su zauna da shi domin su bayyana masa matsayinsu kan lamarin.
Sai dai Barrister Abba Hikima ya nuna cewa har yanzu bai sauya matsayinsa ba, yana mai jaddada aniyarsa ta ci gaba da tafiyar har sai an cimma manufar da aka sanya a gaba.
