Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta Rufe Gidan Talabijin na AIT da Wasu Kafofi 51

Gwamnatin Tarayya ta Rufe Gidan Talabijin na AIT da Wasu Kafofi 51

Date:

Muhammad Bello Dabai

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya, NBC ta janye lasisin gidan talabijin na AIT da Karin wasu kafofi 51.
Shugaban hukumar, Balarabe Ilelah ne ya sanar da hakan yau a Abuja.

Ya alakanta matakin da gazawar kafofin da abin ya shafa wajen sabunta lasisin su, tun daga shekaar 2015.
Baya ga hakan, hukumar na bin kafofin labaran bashin makudan kudi da yakai naira Biliyan 2 da miliyan 6.

Ilelah yace wannan shine rukuni na farko, yayin day a gargadi wasu kafofi da sabunta nasu lasisin, gabanin makamancin wannan mataki ya shafesu.

“Wannan rukunin farko kenan, akwai ragowar wadanda basu biya kudin sabunta lasisi ba a shekarun 2015, da 2016 da kuma 2017. Muna gargadin su kan suzo su sabunta” Inji Ilelah.

Hukumar ta NBC ta baiwa kafofin 52 wa’adin awa 24 daga yanzu, kan su dakaar da aikinsu.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da hukumar ta ci tarar gidan talabijin na Trust TV kudi naira miliyan 5, bias zarginsu da yada labaran yan bindiga ta hanyar basu fifiko.

Tuni dai yan fafutuka suka fara tofa albarkacin bakinsu akan matakin.

Galibi suna kallon hakan a matsayin wani yunkurin na tauye yancin kafafaen yada labarai, da kuma fadin albarkacin baki, wanda suke gani a matsayin barazana musamman a tsarin mulkin dimokradiyya.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...