Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaMatasa uku sun lashe gasar rigakafin allurar Korona da CITAD ta shirya

Matasa uku sun lashe gasar rigakafin allurar Korona da CITAD ta shirya

Date:

Shehu Usman Salihu

 

Matasan da suka shiga gasar wayar da kan al’umma game da muhimmancin karbar rigafin allurar Korona, sun samu kyautar sabon Firinji, Talabijin da Kwamfutar tafi da gidanka.

 

Gasar da cibiyar nan ta CITAD, mai bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta sanya, ya karbi rahotanni daga jihohin Kano, Kaduna, Bauchi, Borno, Flato da Kogi.

 

Da yake zantawa da Premier radio, darakatan cibiyar Injiniya Yunusa Zakari Ya’u, da ya samu wakilcin jami’in shirin Hamza Ibrahim ya ce, sun baiwa matasan horo.

 

Daga jihohin ne da nufin cigaba da wayar da kan alúmma kan muhimmacin karbar rigakafin korona tare da dakile labaran karya da ake yadawa game da cutar.

 

Hamza Ibrahim ya kara da cewa, cikin matasa 18 dake aikin, suna daukan mutum uku ne bayan tantance irin ayyukan da sukayi a duk wata tare da basu kyatuttuka.

 

Wanda a wannan watan, Joseph Aturo yazo na daya da maki 91, yakuma lashe kyautar sabon Firinji, sai Kwaplki Peter Uba daga Jihar Borno da ta zama ta biyu da maki 82, ta lashe kyautar Talabijin din Bango (Plasma) da Hauwa Lawal Kabir daga jihar Flato da tazo ta uku da maki 72, ta kuma samu kyautar sabuwar Kwamfutar tafi da gidanka.

 

Kwaplki Peter Uba daga Jihar Borno da ta zama ta biyu a garsar da ta lashe kyautar Talabijin din Bango (Plasma), ta bayana farin cikinta game da nasarar.

 

Daga bisani Hamza Ibrahim yace ana samar da kyaututtukan ne don kara kwarin gwiwa ga matasan, kuma shirin zai cigaba a kowane wata.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...