Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAtiku ya nemi ayi masa addu'a kar ya kara kiba.

Atiku ya nemi ayi masa addu’a kar ya kara kiba.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya nemi jama’a da suyi masa addu’a kar ya kara kiba.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da yake wallafa rubutu da harshen Hausa.

A cikin wata wallafa da Atiku yayi, ya bayyana yadda aka shirya masa wata liyafa ta ban girma a mahaifarsa dake Adamawa.

Acikin wani salon rubutu na barkwanci Atiku ya nemi alumma suyi masa addu’a kar ya kara kiba.

“A yayin ziyara ta zuwa Adamawa an sake kawata ni tare da wata sabuwar liyafar cin abincin dare a mahaifata dake garin Jada. Ku yi Addu’ar kada na kara kiba kafin na dawo 😀” Inji Atiku.

A baya bayannan dai dan takarar shugaban kasar na PDP Atiku Abubakar na ziyara a jiharsa ta Adamawa a wani bangare na fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2023.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories