37.6 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiKiwon LafiyaDambu yayi sanadiyar mutuwar mutum 7 a Zamfara

Dambu yayi sanadiyar mutuwar mutum 7 a Zamfara

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hafsat Bello Bahara

 

Rundunar Yan Sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutum 7 Yan gida daya bayan sunci wani Dambun Masara.

 

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin a kauyen Danbaza dake karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Kano: ‘Yan sanda sun kama kwayar Tramadol ta naira miliyan 25

Kakakin Rundunar Yan Sandan jihar SP Muhammad Shehu ya bayyanawa kamfanin yada labarai na kasa NAN cewar tuni suka fara binciken makasudin faruwar lamarin.

 

SP Muhammad Shehu yace da zarar sun kammala binciken abinda ke kunshe cikin abincin zasu bayyana sakamakon ga yan jarida.

 

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar makaubcin mamatan da abun ya faru a kan idon shi ya bayyana cewar bayan kammala cin abincin daren nasu na Dambu nan take mutum hudu suka mutu, sauran mutane ukun kuma sun mutu ne yayin da ake basu agajin gaggawa a asibiti.

Latest stories