24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAn kama wani da ke shirin aiko da bindigogi Kano

An kama wani da ke shirin aiko da bindigogi Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

 

Mukhtar Yahya Usman

 

An kama wani mutu a tashar Zuba dauke da bindigogi takwas da ke shirin aikosu Kano.

 

Kungiyar yan sintiri da ke yankin na Zuba ce ta kama mitumin ranar Laraba.

 

A cewar shugaban ‘yan sintirin Yahya Madaki mutumin ya je tashar motar ne da misalin karfe biyu na rana inda yake neman motar da za ta je Kano don bayar da sakon.

‘Yan bindiga sun kai hari kan jami’an immigration a Jigawa

Daga nan ne ya samu direban da ke lodi zuwa Kano ya mika masa sakon da aka sanya a kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai kai wa sakon a Kano.

 

A cewar jaridar Daily Trust an caji mutumin naira dubu 10 kudin dakon kayan, kuma nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi ya ji ko mene ne a cikin kwalin.
Hakan ce ta sanya mutumin ya nemi ya tsere to amma an kama shi.

 

Yahaya Madaki ya ce ko da aka bude kwalin an ga bindiga samfurin AK-47 biyar, sai kananan bindigogi uku.

 

Yanzu haka mutumin na wajen ‘yan sand

Latest stories