33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabarai'Yan bindiga sun kai hari kan jami'an immigration a Jigawa

‘Yan bindiga sun kai hari kan jami’an immigration a Jigawa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar shige da fice a karamar hukumar Birniwa da ke jihar Jigawa.

Shugaban hukumar reshen jihar, ACG Ismail Abba Aliyu, ne ya bayyana hakan ya yin taron maneman labarai a Dutsen jihar Jigawa.

ya ce  ‘yan bindigar sun kashe jami’insu guda daya sannan suka jikkata mutum biyu.

Ya yi ikirarin cewa maharan sun yi wa ma’aikatansa kwanton-bauna a yayin da suke sintiri a hanyar Galadi zuwa Birniwa.

A cewarsa, ‘yan bindigar, wadanda suka kai biyar, sun isa wurin da ma’aikatan shige da ficen ke aiki ne a kan babura sannan suka bude musu wuta.

ACG Aliyu ya bayyana cewa jami’in da aka kashe shi ne Abdullahi Mohammed, yana mai karawa da cewa jami’an da aka jikkata su ne Abba Musa Kiyawa da Zubairu Garba.

Latest stories