Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso ya nada jami'an yada labaran yakin neman zabensa

Kwankwaso ya nada jami’an yada labaran yakin neman zabensa

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya nada Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa da Barrister Ladipo Johnson a matsayin jami’an yada labaran yakin neman zabensa a shekarar 2023 mai zuwa.

 

 

Dr. Abdulmumin Jibril Kofa wanda yake da kwarewa a fannin siyasa yayi digirinsa na daya da na biyu har da na uku a jami’o’in Abuja da Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ha karanci fannin siyasa da alakar kasa da kasa.

 

Jibril Kofa tsohon dan majalisar tarayya ne daga jihar Kano, kuma yanada kwarewar yin hulda da jama’a musamman a sha’anin siyasa.

 

 

Shi kuwa Barrister Ladipo Johnson lauya ne kuma shugaban cibiyar cigaban Kasuwanci da Gudanarwa ta Afirka.

 

Ya yi karatu a jami’ar jihar Legas, kuma tsohon dan takarar Gwamna ne a jihar Legas.

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Ibrahim Adam ya fitar, yace kwankwaso ya bukacesu dasu yaɗa angizon jam’iyyar NNPP a dukkanin sassan Najeriya.

Latest stories

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...