Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniBatanci ga Ma'aiki:Kotun daukaka kara a Kano ta umarci a sake shari’ar...

Batanci ga Ma’aiki:Kotun daukaka kara a Kano ta umarci a sake shari’ar Aminu Sherif

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kotun daukaka kara da ke Kano ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jiha na a koma kotun shari’ar musulunci a sake shari’ar Aminu Sheriff wanda ake zargi da batanci ga ma’aiki cikin wakarsa.

 Idan za a iya tunawa dai an zargi Aminu Sahrif da yin batanci ga ma’aiki cikin wata waka da ya wallafa ya kuma yada ta ta shafinsa na Whatsapp.

A watan Agustan 2020 ne dai babbar kotun shari’ar musulunci da ke Hausawa Filin Hockey ta yankewa Sharif Hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin yin batanci ga ma’aiki.

Alkalin kotun Khalid Muhammad Khani ne ya yanke masa hukuncin karkashin sashi na 382(b) na kundin Penal na 2000.

Sai dai a ranar 21 ga Janairun 2021 ne babbar kotun jiha da ke gidan Murtala ta rushe hukuncin kisan inda ta bukaci a koma kutun a sake sabuwar shari’a.

Wannan na zuwa ne bayan da Sharif ya daukaka kara zuwa kotum ita kuma kotun ta ce an yi masa hukunci ba tare da lauyaba.

Hakan ce ma ta sanya kotun ta ce a koma kotun musulunci a sake sahri’ar bayan an sama masa lauya.

Sai dai wannan hukunci bai yiwa Sharfi dadi ba, da hakan ta sanya ya sake daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Kano.

A zaman kotun na ranar Laraba kotun daukaka karar ta sake yanke hukunci irin wadda kotun bayan ta yanke.

Kotun ta sake cewa a koma kotun shari’ar musuluncin ta Filin Hocky domin sake sabuwar shari’ar.

Shi dai Sharif gudane cikin ‘yan darikar Tijjaniya kuma dan kungiyar Faira, wadanda sune mabiya Ibrahim Inyass, babban malamin addinin musuluncin nan da ke kasar Senegal.

Wakar ta sa dai ta haifar da ce ce kuce a tsakanin danginsa da sauran jama’ar gari da ta sanya sai da ya gudu daga gidansa.

Haka kuma bayan guduwarsa aka samu wasu fusatattun matasa suka bankawa gidan wuta suka keneshi.

Latest stories

Related stories