Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAnyi jana'izar Alhaji Uba Leader a Kano

Anyi jana’izar Alhaji Uba Leader a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fittacen dan kasuwar nan na Kano Alhaji Uba Leader Gwammaja.

Alhaji Uba Leader ya rasu ranar Asabar a wani Asibiti da ke birnin tarayya Abuja.

Ya rasu yana da shekaru 77 a duniya, ya kuma bar matan aure da yaya da dama.

An dai gudanar da jana’izar ta sa ne a masallacin Khalifa Sheikh Ishaq Rabi’u da ke Goron Dutse a Kano.

Jana’izar ta samu halartar dubban mutane da suka hadar da mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamandan Hisbah Sheikh Harun Sani Ibn Sina.

Sauran su ne Abba Kabir Yusuf dan takardar gwamnan Kano a NNPP da sauran manyan mutane.

An dai binne marigayin makabartar yan Tijjaniyya da ke Hajji Camp a Kano.

Latest stories

Related stories