Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMajalisar dokokin Kano ta fara tantance sabbin Kwamishinoni

Majalisar dokokin Kano ta fara tantance sabbin Kwamishinoni

Date:

Aminu Abdullahi

A yaune majalisar dokokin Kano za ta tantance sabbin kwamishinonin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya aike mata don nada su a ma’aikatu daban-daban.

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamna Ganduje ya aikewa da majalisar sunayen mutane takwas da za a tantance tare da amincewa a nada su kwamishinoni.

Haka zalika gwamnan ya sake aikewa da sunan mutum guda a ranar Talata, wanda hakan ke nufin za a tantance mutane tara a matsayin kwamishinonin.

Cikin wadanda za a nada akwai Garba Yusuf Abubakar tsohon kwamishinan kudi zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau.

Sai kuma Lamin Sani Zawiyya da Ibrahim Dan Azumi Gwarzo da Abdulhamid Abdullahi Liman da kuma Ya’u Abdullahi ‘Yan Shana.

Sauran sune Yusif Jibril Rurum da Adamu Abdu Fanda da Saleh Kausani, sai kuma Dakta Ali Musa Burum Burum

Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da wasu kwamishinonin sukayi don tsayawa takara a matakai daban daban a zaben badi dake tafe.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories