Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Tuesday, May 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaGwamnatin Kano ta rufe asibitin Reach clinic

Gwamnatin Kano ta rufe asibitin Reach clinic

Date:

Gwamnatin Kano ta rufe wani asibiti mai suna Reach clinic kwanaki kaɗan da fara aikinsa.

Darakta Janar na hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kan su na jihar, Farfesa Salisu Ibrahim ne ya bayyana rufe asibitin saboda abinda ya kira gaza cika ƙa’idojin aiki da hukumomi suka fitar.

Farfesan ya jaddada cewa an rufe asibitin har sai hukumar gudanarwar ta cika ƙa’idojin bude asibiti ko cibiyar kula da lafiya mai zaman kan ta da aka shimfida.

Farfesan ya kuma tunatar da asibitoci da sauran cibiyoyin kula da harkar lafiya masu zaman kan su a jihar nan, su kiyaye ƙa’idojin da gwamnatin Kano ta gindaya don kare lafiyar al’uma.

Farfesa Salisu ya kuma yi barazanar rufe duk wuraren da aka kama da karya dokar.

Latest stories

Related stories