Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin jihar Kano ta ce kawo yanzu akwai makarantu masu zaman kansu,...

Gwamnatin jihar Kano ta ce kawo yanzu akwai makarantu masu zaman kansu, 5000 daga cikin 7000 da ake da su a jihar nan, wadanda suka ki sabunta rijistar su.

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta ce kawo yanzu akwai makarantu masu zaman kansu, 5000 daga cikin 7000 da ake da su a jihar nan, wadanda suka ki sabunta rijistar su.
Mai baiwa gwamnan Kano shawara kan makarantu masu zaman kansu Kwamared Baba Abubakar Umar ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai.
Baba Abubakar ya ce akwai bukatar dukkanin masu makarantu masu zaman kansu anan Kano, kan su kwana da sanin cewa idan har lokacin da gwamnati ta ware musu domin sabunta lasisin ya wuce basu yi, to kuwa gwamnati bata da matakin dauka face ta ayyana wadanda makarantu a matsayin haramtattu.
Ya ce kawo yanzu akwai masu makarantun 3000 daga cikin 7000 da suka karbi fom din sabunta rijistar su, amma har zuwa yanzu iya 2000 ne suka cike tare da mayar da shi.
Idan mai sauraro zai iya tunawa a baya ne gwamnatin Kano ta sanar da soke duk lasisin makarantun masu zaman kansu, tare da bukatar kowane mai makaranta akan ya sake rijista da gwamnati cewa shine mai makaranta kaza dake dauke da kaza domin gwamnati ta samu damar tattara bayanan da suka kamata kan makarantun masu kansu.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...