Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya goyi bayan tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya tsakanin yankin arewa da kudu, tare da tabbatar da cewa kano za ta ci gaba da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin yin tazarce a zaɓen shekarar 2027.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar motocin yaƙin neman zaɓe guda 50, wadanda waɗanda Chief Oweizide Thomas, wanda aka fi sani da Tompolo ya baiwa jam’iyyar APCn Kano.
Gwamnan ya ce goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu, na da alaƙa da tsarin sauya shugabancin ƙasa daga arewa zuwa kudu bayan ya kammala wa’adin shekaru takwas akan mulki, tare da yin kira ga al’ummar arewacin Najeriya da su kasance masu haɗin kai da haƙuri.
Gwamna Abba ya ce motocin, waɗanda Tompolo, ya bayar, za’a yi amfani da su ne wajen tallafawa harkokin jam’iyyar APC da ƙungiyoyin da ke mara mata baya a ƙananan hukumomi 44 na Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na buƙatar ‘yan siyasa da magoya bayansu da su gudanar da yaƙin neman zaɓen 2027 cikin zaman lafiya, tare da mayar da hankali kan manufofi da tsare-tsaren ci gaban al’umma, gujewa tashin hankali, aikata laifuka da ɓata sunan mutane.
