Saurari premier Radio
40.7 C
Kano
Wednesday, May 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGasar Wasannin Motsa jiki ta 2023:Jihar Kano ta samu lambobin yabo na...

Gasar Wasannin Motsa jiki ta 2023:Jihar Kano ta samu lambobin yabo na Zinare 18

Date:

Ahmad Hamisu Gwale-Abuja

Tawagar Jihar Kano a gasar Motsa Jiki ta masu bukata ta musamman ta kasa, ta samu lambobin yabo na Zinare 18 a gasar da aka buga a birnin tarayya Abuja.

Jihar Kano ta fafata a wasanni 12 cikin 15 da aka gudanar a gasar, wadda ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa ta shirya a karo na biyu a tsakanin Jihohin Najeriya.

Yan wasa da dama daga bangarori daban-daban da suka halarci gasar ne suke nuna bajintar lashe Sarkokin Zinare, Azurfa da kuma Tagulla a gasar da aka tsara daga 8 zuwa 14 ga Disambar 2023 gasar da fafata a filin wasa na Moshood Abioloa da ke birnin tarayya Abuja.

Wasu cikin Yan wasan Kano sun lashe Lambobin Zinare, Azurfa da kuma Tagulla ciki har da dan wasan Kano Ibrahim Abubakar wanda ya lashe Zinare a harbin Mita 10 na Maza.

Itama Bilkisu Isyaku Ibrahim daga tawar Kano, ta lashe lambar yabo ta Zinare a harbin Mita 10 na Mata.

Haka Zalika dan wasan Kano Gbengay Osinowo ya lashe Zinare shima a wasan Para Table-Tennis.

Sauran sune Shafat Dauda, Seun Opawole da Ihueze Victoria da Musa Bala, Abdullahi Muhd, Ezurike Roland da Anouluwapo suma duka sun lashe Lambobin yabo na Zinare.

Haka zalika akwai Adeleke Abejoye Odunay, Adewale Sefih, Sulaiman Taiwo, Aromomse Suliat suma sun samu nasarar lashe Wadannan lambobin yabon na Zinare…

A gefe guda ma jihar Kano ta kuma lashe Lambobin yabo na Azurfa 13, baya ga lashe Lambobin Tagulla 17 a gasar da aka fafata birnin tarayya Abuja.

Shin wanne Kalubale tawagar jihar Kano ta fuskanta a gasar?

Tawagar Kano ta fuskanci kalubale na kwam gaba kwam baya tare da rashin samun kudin gudanar da aiyyukan gasar, lamarin da ya sanya aka shiga halin rashin tabbas.

Wakilinmu ya tabbatar mana cewa, bisa rahotanni da ya samu daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da sai da komai ya tsaya cik , sakamakon rashin kudin Inda ake kyautata zaton wasu daga cikin ‘yan wasan sunyi yunkurin bara zana ta yin bore dangane da halin da suka shiga .

Suma kansu wasu cikin jami’an Hukumar wasanni ta jihar Kano (KSSP) da masu lura da Yan wasa (Helpers) da masu horar sa da yan wasan dama jami’an Lafiya duka sai da suka shiga halin rashin tabbas sakamakon rashin kudaden Alawus.

Shin mai ya faru da Yan Jarida?

Suma ‘yan Jaridun da suke tare da tawagar su sama da 10 sai da suka shiga mawuyacin hali, bisa yadda suka samu kansu a yanayin da babu wani cikin jami’an hukumar wasanni ko a gwamnatin jihar Kano da ya yi musu karin haske kan halin da aka shiga.

Cikin rahotannin Sirri da ‘yan Jaridun daga kafafen yada labarai da dama suka gudanar, sun gano an samu rarrabuwar kai da rashin tsara gudanar da aikin tawagar ta jihar a gasar.

Har wa yau, sai da ‘yan Jaridun su kayi bakin kokarin su don Jin ya akayi aka haihu a ragaya daga bangaren Gwamnati, sai dai hakan su ya gaza cimma ruwa sakamakon Babu wanda ya yarda ya yi magana kan lamarin da tawagar ta tsinci kanta ciki.

Tin da fari kafin tawagar ta taso zuwa wasan masu bukata ta musamman a Abuja, jami’an hukumar wasannin sun tabbatar dacewar gwamnatin jiha ta sahale kudaden da za a gudanar ayyukan tawagar wanda aka alkarwartawa dukkanin masu ruwa da tsaki a tafiyar cewar za a sallame su da zarar an sauka a Abuja, a Ranar Litinin din da ta gabata.

Abin da ya sanya har zuwa Daren ranar Alhamis babu ko da Labarin sisin Kwabo da ya shigo dangane da Alkawarin na baya da Gwamnatin jihar Kano ta yi.

Mai ya faru daga baya?

Bayan Yan Jaridu sunyi aikinsu na yada irin abubuwan da suka faru tuni a ranar Alhamis ranar karkare gasar aka jiyo Gwamnatin Kano ta ce zata biya kowa hakkin sa.

Mai rikon shugabancin hukumar wasanni ta Jihar Kano Malam Bala Sani Shehu ne ya bayyana hakan a tattauna da manema Labarai.

Yana mai cewa kudaden Alawus-Alawus din tawagar Kano Gwamnatin Kano za tayi kokari gama biya kafin ranar Larabar mako mai zuwa ta watan Disambar 2023.

Yana mai cewa kawo yanzu haka an kashe kimanin kudi Naira Miliyan Tara daga cikin Miliyan Talatin da Gwamnatin Kano ta warewa tawagar domin kudin Rigista, dana Abinci da mai na Motoci da kuma kudaden Yan Jaridu da sauran wakilai daban-daban.

Latest stories

Hajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa Saudiyya

Mukhtar Yahya Usman A yau Laraba ake sa ran fara...

Sheik Abduljabbar Kabara ya sake korar Lauyansa.

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin...

Related stories

Hajjin Bana: Yau Laraba za a fara jigilar alhazan kasar nan zuwa Saudiyya

Mukhtar Yahya Usman A yau Laraba ake sa ran fara...

Sheik Abduljabbar Kabara ya sake korar Lauyansa.

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin...