Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiECOWAS Ta Dakatar Da Jamhuriyar Nijar Daga Kungiyar

ECOWAS Ta Dakatar Da Jamhuriyar Nijar Daga Kungiyar

Date:

Kungiyar kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ta dakatar da jamhuriyar Nijar daga cikin ta tare da amince wa da juyin mulkin sojojin kasar suka yi har sai lokacin da aka koma amfani da kundin tsarin mulki.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taron shugabanninta da ya gudana a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ce ta fito karara ta bayyana gamsuwa da cewa sojoji sun yiwa Bazoum juyin mulki, don haka a yanzu za’a mu’amalanci kasar ne a matsayin wadda sojoji suka kwaci mulki ta karfi.

A baya dai kungiyar bata amince da juyin mulki ba, in take ganin wasu mutane ne kawai suka yi garkuwa da hambaraarren shugaban kasar Bazoum Muhammed da kuma watsi da kundin tsarin mulki.

ECOWAS ta bukaci sojojin da su gaggauta mayar da mulki ga farar hula tare da sakin shugaban kasar da suke rike da shi.

Tuni dai jagoran juyin mulkin, Abdourahmane Tchiani, ya yi watsi da wannan bukata, in da ya ce babu wata kasa da zata tsarawa Nijar din abinda za ta yi.

Latest stories

Related stories